BBC navigation

Wani harin bam a Syria ya halaka mutane da yawa

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:10 GMT
Wani harin bam a Syria

Wani harin bam a Syria

Mutane da dama sun mutu sakamakon harin Bam a Damascus babban birnin kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran Syria-SANA ya ce, fashewar bam din ya auku ne a arewa maso yammacin kasar, amma kuma ba a bayyana adadin wadanda suka rasu ba.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Syrian Observatory for Human Rights dake nan London, ta ce wasu bamabamai uku sun fashe a yankin, kuma akalla mutane 10 ne suka gamu da ajalinsu.

Yankin ya kasance inda 'yan shi'a Alawi masu goyon bayan shugaba Assad suke da rinjaye.

Wakilin BBC ya ce dakarun gwamnatin Syria suke da iko a sararrin samaniyar kasar, kuma sun shirya amfani da wannan abu don samu galaba akan 'yan adawa.

Wannan ne karo na biyu da aka samu tashin bamabamai a Damascus cikin kasa da kwanaki biyu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.