BBC navigation

Pirayim Minista Cameron ya ce dole Shugaba Assad ya sauka daga karagar mulki

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:28 GMT
Pirayim Minista Cameron da yan gudun hijirar Syria

Pirayim Minista Cameron da yan gudun hijirar Syria

Pirayim Ministan Birtaniya, David Cameron ya ce, Birtaniya za ta soma tattaunawa da 'yan tawayen Syria dake dauke da makamai domin su dunkule wuri guda wajen yakar shugaba Bashar Al Assad.

David Cameron ya sauka ta jirgin sama mai saukar ungulu a kan iyakar Jordan da Syria, tare da jami'an tsaron Jordan sun tsaya suna kallon kasar Syria daga kan iyaka.

Jami'an Jordan din sun shaida masa cewa, a kullum 'yan gudun hijra daga Syria 500 na tsallakowa kasar su, inda daga bisani kuma Pirayin ministan ya gana da wasu daga cikin su.

A sansanin 'yan gudun hijra na Za'atari inda yaran Syria suka rera masa waka, Mr Cameron ya yi kira ga Shugaba Assad da ya sauka daga kan mulki ko ta halin kaka.

Ya kare manufar Birtaniya ta kin baiwa 'yan tawaye makamai, sai dai ya ce Birtaniya na kara kokari wajen kai dauki ga mutanen da ke cikin wani mawuyacin hali, saboda tana son zama kasa ta biyu bayan Amurka wajen bada agaji mai yawa.

Ya ce muhimmin abinda zai sa a gaba yanzu shi ne, tataunawa da shugaban Amurka da aka sake zaba a kan hanyoyin da ya kamata kasashen yamma su bi wajen kara taikawa al'ummar Syria da ke cikin mawuyacin hali.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.