BBC navigation

Halin da fararen hula ke ciki a Syria yayi muni --Inji Kungiyar Red Cross

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:32 GMT
Yan gudun Hijirar Syria

Yan gudun Hijirar Syria

Shugaban kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ko Croix Rouge, ya ce yanzu halin fararen hula ke ciki a Syria, ya munin gaske ta yadda abun yana neman ya fi karfin kungiyar.

Peter Maure ya ce jami'an kungiyar ta Red Cross ba sa iya cimma dukan sassan kasar.

Ya ce,"duk da cewa muna yawaita ayyukanmu a kasar, amma al'ammari yana neman gagarar mu, saboda halin da ake ciki yana kara kazancewa saboda fadan da ake cigaba da yi."


A halin da ake ciki kuma, Babbar kungiyar adawa ta Syria, watau Syrian National Council ta zabi mamobin kwamitin gudanarwarta su 40, kuma galibinsu masu ra'ayin Islama ne.

Sai dai babu mace ko da daya a cikin kwamitin gudanarwar. Kungiyar wadda ta ke taronta a birnin Doha na Qatar, ta ce za ta zabin shugabanta a gobe Jumaa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.