BBC navigation

Frayin Ministan Birtaniya na karbar bakuncin taro kan talauci

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:18 GMT
Matsalar talauci a Afirka

Matsalar talauci a Afirka

Idan an jima a yau ne Frayin Ministan Birtaniya zai yi wani taro a fadarsa dake Dawning Street, kan yadda ya kamata duniya ta tunkari matsalar fatara a shekarun dake tafe.

Ya na daya daga cikin shugabannin dake jagorancin tawagar Majalisar Dinkin Duniya ciki har da shugabar kasar Liberia da kuma shugaban kasar Indonesia.

Wannan batu ne da ya shafi kasashe matalauta, to amma a cikin gida, batu ne mai sarkakiya, inda wasu a cikin jamiyyarsa ta Conservative ke cewa, tallafin da Birtaniya ke bayarwa ya yi yawa.

Su dai wadannan muradu, Majalisar Dinkin Duniya ta bullo da su ne a farkon wannan karni, kuma ana sa ran a wannan lokaci ne aikinsu zai kare.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.