BBC navigation

Za a samarwa matasa aiki a Damagaram

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:46 GMT

A Jamhuriyar Nijer wani kwamitin wayar da kan jama'a kan ayyukan Shugaba Mahamadou Issoufou ya cimma yarjejeniya da matasan birnin Damagaram game da yadda za a kawo karshen yawan tarzomar da ake samu a birnin.

Kwamitin ya ce za a samarwa matasan ayyukan yi domin kawo karshen ayyukan ashsha a birnin -- tsarin da matasan su ka yi marhabin da shi.

Matasan na Damagaram sun amince cewa su na tabka barna da hadassa asara a birnin, wanda shine na biyu mafi girma a Jamhuriyar ta Nijar. To amma sun ce da zaran gwamnatin Shugaba Mahamadou Issoufoun ta saman masu ayyukan yi ba wani danyen aikin da za a sake yi a birnin.

Matassan sun yi wannan furucin ne yayinda su ke taro da kwamitin dake kokarin samar da goyon baya ga ayyukan Shugaba Issoufou a jiya a dakin shawara na Makarantar Horon Malaman Jinya ENESP na Damagaram.

Mallam Aboubakar Souleymane Dan Bouzouwa, magatakardar matasan, ya ce idan matasa sun samu aikin yi, ba za su samu lokacin aikata abubuwa marassa kyau ba.

Jami'an kwamitin dai sun baiwa matasan tabbacin cewa za a samar masu ayyuka.

Sun ce tuni aka shirya tsarin tallafa masu a harkar ilmi da kuma basu horo a fannin sana'o'i dabam dabam.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.