BBC navigation

Amnesty ta zargi sojin Nigeria da cin zarafi

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:53 GMT
barnar harin Boko Haram

barnar harin Boko Haram

Kungiyar kare hakin bil'adama ta Amnesty International ta ce jami'an tsaro a Nigeriya kan wuce gona da iri a fadan da su ke yi da kungiyar Jama'atu Ahlus sunna Lidda'awati wal Jihad wadda aka fi sani da suna Boko Baram.

A rahoton da kungiyar ta fitar a yau, Amnesty International ta ce jami'an tsaron kasar na amfani da karfin da ya wuce kima wajen maida martani kan hare-haren da kungiyar Boko Haram ke ikirarin kaiwa, abun da kuma ke dagulawa da kuma janyo tabbabarewar al'amura.

Amnestyn ta ce suna gana ma jama'a azaba da kisa ba tare da shari'a ba, da kone gidajen mutane da kuma tsare mutane ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba.

To saidai wani kakakin sojin Nijeriyar ya musanta zargin da ake yi musu ya na cewar, duk abinda su ke yi su na yin su ne bisa doka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.