BBC navigation

Majalisar Nigeria na shirin gyara ga kundin tsarin mulki

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:28 GMT
Taswirar Nigeria

Taswirar Nigeria

A Najeriya, majalisar dokokin kasar ta fara bin matakan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Daya daga cikin muhimman batutuwan da aka bayyana ra'ayoyi kan su ya zuwa yanzu, shi ne batun sama wa majalisun dokoki na jihohi da kananan hukumomi 'yancin karba da sarrafa kudaden da akan ware masu.

Wasu kungiyoyin farar hula da kwararru, har ma da wadanda suke cikin sha'anin mulki, suna ganin muddin majalisun dokokin da kananan hukumomin ba su sami wannan 'yanci ba, to wadannan bangarori biyu za su cigaba da gaza gudanar da ayyukansu yadda ya dace.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.