BBC navigation

Obama da Romney sun koma kampe gadan-gadan

An sabunta: 1 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:20 GMT
romney da obama

Mitt Romney da Shugaba Barack Obama

Shugaba Barack Obama ya kome ga yakin neman zabensa, wanda ya jinginar saboda mahaukaciyar guguwar da ta yiwa gabar tekun gabacin Amurka kaca-kaca.

Abokin karawarsa na Jama'iyar Republican, Mitt Romney, shi ma yana ci gaba da nashi yakin neman zaben.

Kuri'un jin ra'ayoyin masu zabe na ci gaba da nuna cewar takarar nada kusanci matuka, to amma dai masu aiko da labarai sunce mai yiwuwa yadda Shugaba Obama ya tinkari matakan shawo kan barnar mahaukaciyar guguwar ya karfafa damarsa.

Obama yana gangami ne a jihohi uku da suke da muhimmanci wajen ganin wanene zai zama shugaban kasa a zabe na gaba, wato Wisconsin, Nevada da Colorado.

A yayinda babban mai kalubalantarsa Mitt Romney yake na sa gangamin jihar Vaginia.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.