BBC navigation

Gwamnatin jihar Orissa a India ta ci wasu kamfanoni 20 tara mafi girma

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:47 GMT
India

Kamfanonin na hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a India

Gwamnatin jihar Orissa dake Gabashin India ta ci wasu kamfanoni 20 tarar da ba a taba ganinta irin ta ba, ta fiye da dala biliyan 10, saboda sun hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba tun shekara ta 2001.

Kamfanonin sun hada har da kamfanoni mafi girma a India, kamar su Tata da Jindal.

Kamfanin na Tata zai biya tarar dala biliyan 6 shi kadai.

Ana sa ran kamfanonin, wadanda gabilinsu suke hako ma'adanin karfe, za su daukaka kara.

Masu sukar lamirin gwamnati sun ce gwamnatin jihar ta Orissa ta dauki matakin ne kawai, bayan da wani rahoto da gwamnatin kasar ta sa aka hada a kan illar aikin hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba a jihohin kasar da dama.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.