BBC navigation

An shiga karancin makamashi a Amurka

An sabunta: 2 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:08 GMT
Mahaukaciyar guguwar Sandy a Amurka

Mahaukaciyar guguwar Sandy a Amurka

Kwanaki 5 bayan da mahaukaciyar guguwar nan hadi da ruwan sama ta Sandy ta haddasa mummunar barna a wasu sassa na Gabar ruwa ta Arewa maso Gabashin Amurka, akwai alamun cewa jama'a na kara harzuka game da karancin makamashi a yankin.

An yi ta samu dogayen layuka a gidajen mai, kuma ma'aikata na kokarin maido da wutar lantarki ga miliyoyin jama'a.

Mutane fiye da 100 ne aka tabbatar cewa sun hallaka a Amurka a sakamakon mahaukaciyar guguwar ta Sandy.

A yankin Staten Island dake birnin New York, daga cikin mutanenda suka rasu har da wasu 'yan uwa biyu da mai shekaru biyu da dan shekaru hudu, wadanda ruwa ya kwace su daga hannun mahaifiyarsu.

A wasu yankunan birnin, wasu mazauna unguwanni sun fara komawa gidajensu.

wakiliyar BBC ta ce wasu mazauna yankunan dake gabar teku a New Jersy sun fara tantance irin asarar da suka yi, inda wasu daga cikinsu suka rasa dukkanin abubuwanda suka mallaka, wasu kuwa suna ta kokarin kwaso kayayyakinsu da ruwa ya shanye, inda suke sa ran samun wani abu daga ciki.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.