BBC navigation

An soke wasan gudun yada kanin wani a Amurka

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:43 GMT

Wasan gudun yada kanin wani

An soke wasan gudun yada kanin wani na Birnin New York.

Soke wasan ya biyo bayan suka da akayi cewa zai iya kawo katsalandan kan kokarin share karikicen da mahaukaciyar guguwan nan Sandy ta haddasa a arewa maso gabacin Amurka.

'Yan wasan sama da dubu arba'in ne daga sassa daban daban na Duniya suka hallara don yin gasar.

Masu wasan dai na yin layin rigista lokacin da labari ya isa garesu cewa an fasa wasan, wasu na cewa ba ayi musu adalci ba; wasu kuwa na nuna kaduwar su da labarin.

Masu shirya gasar dai na ganin yin gasar wata hanya ce da za a samu kudaden shiga da za a iya amfani da su wajan farfado da asarar da mahaukaciyar guguwar ta haifar.

Izuwa yanzu dai har sun hada kusan dala miliyan uku.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.