BBC navigation

An hana dakarun wanzar da zaman lafiya shiga Darfur

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:02 GMT

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Darfur

Dakarun kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur na Sudan sun ce sojoji sun hana su zuwa wurin da aka ce an kai wani hari inda aka kashe mutane goma a ranar Juma'a.

Dakarun na Tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya sun ce masu makoki sun kai gawarwakin mutane goma hedikwatar wakilan Majalisar Dinkin Duniyar da ke birnin el Fasher, suna cewa an kashe su ne a wani hari da aka kai a jihar Darfur ta arewa.

Har yanzu ba a tantance wanda ke da alhakin kai harin ba.

Ana ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a yankin Darfur duk da samun 'yancin kai da Sudan ta Arewa ta yi a shekarar da ta gabata.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.