BBC navigation

Nijar: an sako ma'aikatan agaji 5 da aka sace

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:51 GMT

Muhammadu Issofou, shugaban Nijar

An saki ma'aikatan agajinnan su biyar da aka sace watan jiya a janhuriyar Nijar, kuma abokin aikinsu na shida da aka harba a lokacin da ake kokarin garkuwa da su ya mutu sanadiyyar raunukan da ya samu.

Ma'aikatan agajin waɗan ɗa 'yan Nijar ne da kuma ɗan Chadi sun ce an kai su arewacin Mali ne inda 'yan ƙungiyar masu kaifin kishin Islama suka tsaresu.

Tuni dai ƙungiyoyin agajin na BEFEN ta Nijar da kuma Alerte Sente ta Chadi suka tabbatar da sako jami'an na su.

Matsalar sace mutane dai ta ƙaru a yankin tun bayan da a farkon wannan shekarar ƙungiyoyiin masu kafin kishin Islama suka ƙwace iko da arewacin Mali bayan juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.