BBC navigation

Faɗa ya ƙazanta a Syria

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:58 GMT

Yaƙi a Syria

An kwashe dukkan tsawon ranar yau dinnan ana gwabza kazamin fada tsakanin dakarun 'yan tawayen Syria da na gwamnati a kewayen wani muhimmin sansanin sojin sama dake arewacin ƙasar.

Harin da 'yan tawayen suka kai kan sansanin sojin dake Taftanaz an kai shi ne da nufin taƙaita ci gaba da amfani da ƙarfin da gwamnatin ke yi ta sama.

'Yan tawayen sun ce suna amfani da tankunan yakin da suka kwace a harin da suke kaiwa.

Rahotannin na cewa an tura karin sojojin gwamnati da zasu dafawa waɗanda ke wajen.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.