BBC navigation

Amurka: Yaƙin neman zaɓe ya zafafa

An sabunta: 3 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:18 GMT

Romney da Obama

Yayin da ya rage 'yan kwanaki gabanin zaɓen shugaban ƙasar Amurka, Shugaba Obama da abokin hamayyarsa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney, na ta yin jawabi ga dimbin mutanan da suka yi dafifi a gangamin yaƙin neman zaɓen da suke yi a wasu jihohin ƙasar.

Dukka 'yan takarar biyu na ta hanƙoron kame muhimman jahohin da a nan ne za su ci zaben ko akasin hakan.

A jihar Ohio, shugaba Obama ya faɗawa taron gangamin cewa an samu ci gaba a ƙasar amma har yanzu da sauran aiki. Yayin da shi kuma Mr Romney ya faɗa a wajen gangamin da ya yi a New Hamshire cewa yana son jagorantar masu kaƙa ƙuri'a zuwa ga kyakykyawar makoma.

Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a dai ta nuna 'yan takarar biyu na tafiya kafaɗa da kafaɗa, sai dai kuma Mr Obama ya ɗan fi ƙarfi a muhimman jahohin da ake fafatawa a kansu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.