BBC navigation

Masar: An zaɓi sabon Paparoman Kibɗawa

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:48 GMT

Sabon Paparomna Kibɗawan Masar

Cocin Kibɗawa a ƙasar Masar ya zabi sabon Paparoman da zai jagoranci mabiya addinin kirista na ƙasar da aka ƙiyasce yawansu ya kai miliyan takwas.

Bishop Tawadros, mai shekaru sittin, tsohon mataimakin aparoma Shenouda na uku ne, wanda ya rasu a watan Maris bayan ya kwashe shekaru araba'in a kan muƙamin.

Wani yaro da aka rufewa ido ne ya zaɓi sunan sabon Paparoman a wajan wani babban taron addu'o'i da akai a majama'ar Saint Mark dake birnin Alƙahira.

An dai zaɓi sabon Paparoman ne a daidai lokacin da Masar ke fuskantar sauye-sauye ta fuskar siyasa da zamantakewa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.