BBC navigation

Kano: 'Yan bindiga sun kashe mutane uku

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:19 GMT

Taswirar Najeriya

Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nigeria na cewa wasu yan bindiga sun kashe mutane uku a unguwar Hotoro.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau yayin da yan bindigar suka buɗe wuta a kan mutanen, inda nan take suka riga mu gidan gaskiya.

Runudunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da lamarin, inda ta ce biyu daga cikin mutanen ma'aikatan kamfanin gine gine ne na Dantata and Sawoe.

Wannan hari dai na faruwa ne bayan an samu 'yar sararawar hare-hare a birnin na Kano.

Jihohin arewacin Najeriya da dama ne dai ke fama da hare-hare da wasu lokuttan kungiyar da ake kira Boko Haram ke ikirarin kaiwa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.