BBC navigation

An kafa sabuwar majalisar zartarwar Somalia

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:02 GMT
Shugabannin kasar Somalia

Shugabannin kasar Somalia

Sabon Firayim Ministan Somalia, Abdi Farah Shirdon, ya bayyana sunayen ministocinsa, wanda a karon farko aka sa mace a matsayin ministar kula da harkokin waje, wato Fauzia Yusuf Haji Adan.


An kuma nada wata macen, Maryam Qasim a matsayin ministar kula da kayutata rayuwar jama'a, wanda wani babban aiki ne a kasar da aka kwashe shekaru 20 ana yaki ga kuma fari da yunwa da suka daidaita.


Majalisar zartarwar dai bata kai ta yawan ta baya ba, inda yanzu take da mambobi goma kawai.

Masu aiko da rahotanni sun ce da kyar majalisar zata amince da sabuwar gwamnatin sabilida wasu haulolin da ganin ba'a basu wakilcin da ya kamata ba.


A kwanannan ne aka zabi sabon shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin Somalian, inda aka kwashe shekaru 20 babu wata cikakkiyar gwamnati.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.