BBC navigation

'Yan adawar Syria na kokarin hada kansu

An sabunta: 4 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:48 GMT
Manyan 'yan adawar Syria

Manyan 'yan adawar Syria

Kungiyoyin 'yan adawar Syria sun fara wasu jerin tarurruka a Qatar dan kokarin hada kan shugabanninsu kuma daga bisani su kafa wata gwamnatinsu a wajen kasar.

Babbar kungiyar 'yan adawar ta Majalisar kasa ko kuma Syrian National Council wadda ta kunshi manyan 'masu ilimi da wadanda ke gudun hijira na tattaunawa na kwanaki 4 da nufin kawo kananansu kusa da abubuwan da ake yi a kasa.

Nan gaba a cikin makonnan ne kuma za su duba yiwuwar amincewa da wata shawara da Amurka ke goyan baya ta kafa wata sabuwar tawagar shugabanni mai mambobi 50 da za ta kunshi karin wakilai daga cikin Syria.

A wani labarin kuma wani harin bam da akai kai a tsakiyar birnin Damashka na kasar Syria ya jikata mutane da dama dake kusa da ginin shelkwatar sojojin kasar.

Gidan talabijin din kasar ya dora alhakin harin bam din wanda ya tashi a wata mota kan 'yan ta'adda.

Wannan harin yazo a dai dai lokacin da ake ci gaba da gumurzu a duk fadin Syria, da suka hada da hare haran da jiragen sama ke kaiwa a wajan birnin Damashka.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.