BBC navigation

Jajiberen zaben shugaban Amurka

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:07 GMT

Obama da Romney

Shugaban Amurka Barack Obama da abokin hamayyarsa na jam'iyar Republican, Mitt Romney, na kara matsa kaimi inda suke samun goyon bayan wadansu fitattatun mutane da ke nema musu kuri'u a yakin neman zaben da ake kan-kan-kan tsakanin 'yan takarar.

Mista Obama ya fita yakin neman zabe a jihar New Hampshire shi da tsohon shugaba Bill Clinton, inda fitaccen mawakin nan na kasar, Stevie Wonder da wadansu mawakan suka taya shi yakin neman zabe a jihar Ohio

Mista Romney ma ya ci gaba da yakin neman zabe don neman kuri'un masu zaben da ba su yanke shawara kan dan takarar da za su zaba ba, inda ya jaddada cewa zai samar da shugabanci na gari a kasar.

Hakan dai na faruwa ne a daidai lokacin da hukumomi a kasar ke kokarin samar da gidaje ga dubban daruruwan mutanen da suka rasa muhallansu sanadiyar mahaukaciyar guguwar da ta aukawa kasar a makon jiya, domin gujewa wani muku-mukun sanyi da wata tsawar da ke shirin fadawa kasar a makon gobe.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.