BBC navigation

Haiti ta bukaci tallafin gaggawa

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:25 GMT

Barnar da mahaukaciyar guguwa ta yi a Haiti

Firayim Ministan kasar Haiti, Laurence Lamothe, ya yi kira ga kungiyoyin kasashen duniya da gwamnatoci su kai wa kasar daukin gaggawa saboda mummunar barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Sandy ta yi wa kasar.

Tun farko, hukumomin agaji sun nuna damuwar su a kan barnar da guguwar ta yi wadda ta hallaka fiye da mutane hamsin a can.

Mahaukaciyar guguwar ta lalata amfanin gona tare da wanke gidaje na dubban 'yan kasar ta Haiti.

Hukumomin agaji sun ce akwai fargabar da ake da ita ta yaduwar cutar kwalara a yankunan da aka samu ambaliyar ruwa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.