BBC navigation

Nijar: Yadda ci-rani a Amurka ke kashe aure

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:59 GMT

Matan jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar, wadansu mata da mazajensu ke zaune a kasar Amurka don ci-rani na kokawa saboda rashin komawar mazajen nasu gida a kan lokaci, lamarin da ke hadassa mutuwar aure a lokuta da dama.

Akasarin matan da BBC ta tattauna da su sun ce mazajen nasu sun kwashe shekara-da-shekaru a Amurka ba tare da dawowa ba.

Lamarin dai kan sanya mutuwar aure da dama.

Hajiya Hajara na cikin matan da BBC ta yi hira da su; ta ce mijinta ya tafi Amurka shekaru goma sha biyar da suka gabata amma har yanzu bai dawo ba.

A cewarta,''Tun da ya tafi Amurka shekaru 15 da suka wuce bai dawo ba, har na gaji da zama amma iyaye na sun ki yarda a kashe aure na da shi''.

Matan sun ce duk da yake mazajen na aiko musu da kudin kashewa, ba sa gamsuwa idan ba mazajen ne suka dawo ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.