BBC navigation

An kashe yarinya saboda 'kallon maza' a Pakistan

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:58 GMT
An daure iyayen Anusha  saboda kisan da suka yi mata

Iyayen Anusha

Wadansu iyaye da ake zargi da kashe 'yar su matashiya ta hanyar watsa mata guba sun gaya wa BBC cewa sun yi mata horon ne saboda sun yi imanin cewa za ta kawo kaskanci a gare su.

An kame iyayen ne, mata da miji, a yankin Kashmir da ke karkashin mulkin Pakistan a makon jiya bayan an samu 'yar su Anusha da kunar da ta shafi kashi sittin bisa dari na jikinta.

Mahaifin yarinyar ya shaida wa BBC cewa an yi wa Anusha horon ne saboda ta kalli wani yaro.

Ya ce: "Akwai wani yaro da ya wuce a kan keke, Anusha ta waiwaya ta kalle shi har sau biyu. Na gaya mata kada ta kalle shi, saboda bai dace ba."

Mahaifiyar kuma ta ce Allah ya kaddara Anusha za ta mutu ne a hannunsu.

Mata da 'yan mata da dama suna rasa rayukansu a hannun 'yan uwansu a kowacce shekara a kasar ta Pakistan saboda dalilai irin wadannan.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.