BBC navigation

An nada sabon ministan cikin gida na Saudiyya

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 19:46 GMT
Sarki Abdallah na Saudiyya

Sarki Abdallah ya nada sabon ministan cikin gida

Sarki Abdallah na Saudi Arabia ya cire ministan cikin gidan Kasar tare da maye gurbin- sa da mutumin da yake tafiyantar da harkokin tsaron kasar shekara da shekaru

Sabon Ministan dai shine Yarima Mohammed bn Nayif, dan Marigayi Yarima Nayif wanda ya rasu a watan Yuni bayan da shi kansa ya rike mukamin Ministan cikin- gidan tsawon shekaru

Yarima Mohammed ya maye gurbin Yarima Ahmed bn Abdul aziz, daya daga cikin kannan Sarkin, wanda ya rike mukamin na wasu 'yan watanni

Wakilin BBC yace wata dokar gidan sarauta ce ta sanar da cewa an cire shine daga kan mukamin- nasa bayan da ya bukaci yana son hakan

Kuma abu mafi mahimmaci ga sabon ministan shine cewar shekarun sa hamsin da 'yan kai, wata alama ke nan dake nuni da cewar Kasar Saudiyyan maiyiwuwa daga karshe tana shirin samar da wani karni na matasa a matsayin shugabanni

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.