BBC navigation

Zaben shugaban kasar Amurka ya karato

An sabunta: 5 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:17 GMT
'Yan takarar shugaban kasar Amurka

'Yan takarar shugaban kasar Amurka

Shugaba Barack Obama da mai kalubalantar sa na jam'iyyar Republican, Mitt Romney na rangadi na karshe zuwa wasu jahohin kasar masu mahimmanci, a rana ta karshe ta yakin neman zabe, kafin zaben shugaban kasar da za a gudanar ranar talata.

Shugaba Obama zai je Wisconsin da Iowa da kuma Ohio.

Mitt Romney kuwa zai rankaya ne zuwa wasu jahohi hudu da suka hada da Ohio.

Mutanen biyu dai na tafiya kusan kafada da kafada da juna a kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta duk kasar.

To batun bakin haure dai na daga cikin wadanda ake muhawara a kansa tsakanin 'yan takarar biyu a zaben.

Wani yunkuri da shugaba Obama ya yi a baya na kawo gyara ga dokar shige da fice ya ci karo da koma-baya, bayan da 'yan adawa na jam'iyyar Republican suka ki mara masa baya.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.