BBC navigation

Najeriya: Kamfanoni wayar salula sun koka

An sabunta: 7 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:06 GMT

Taswirar Najeriya

Ƙungiyar kamfanonin wayar salula a Najeriya sun ce, masu amfani da layukansu zasu cigaba da fuskantar tangarɗa saboda hare-haren da ake kaiwa turakan sadarwarsu a arewacin Najeriya da kuma ambaliyar ruwa.

'Yan ƙungiyar sun kuma koka da cewa, haraji kala-kala da ake aza musu yasa a wasu jihohi ana rufe turakan sadarwarsu.

Sun kuma yi kukan cewa, hare-haren da ake kaiwa zasu ci gaba da kawo tangarda ga sadarwa da wayar salula musamman ma jihohin arewacin Najeriya.

Sai dai sun ce, zasu ci gaba da yin iyakar ƙoƙarinsu wajen warware wannan matsala.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.