BBC navigation

An ba da umarnin sanyawa Haqqani takunkumi

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:42 GMT

Wadansu 'yan kungiyar Haqqani

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da umurnin sanya takunkumi na kasashen duniya a kan kungiyar 'yan ta'adda ta Haqqani wadda aka dora wa laifin hare-hare da dama da aka kai a kan ofisoshin gwamnati da na kungiyar tsaro ta NATO a Afghanistan.

Da ma kungiyar Haqqani da babban mai shirya hare-haren kunar bakin-waken da 'yayanta ke kai wa, Qari Zakir, suna fuskantar yiwuwar kwace musu kadarori da haramcin tafiye-tafiye da kuma na samun makamai.

Ana kallon 'ya'yan kungiyar, wadanda ke da alaka ta kut-da-kut da kungiyar Taliban, a matsayin mafiya hatsari cikin kungiyoyin da ke yakar gwamnatin Afghanistan da kuma dakarun kungiyar tsaro ta NATO.

Amurka ta yi maraba da wannan mataki da Kwamatin Sulhun Majalisar Dinkin Duniyar ya dauka.

A watan Satumba ne Amurka ta sanya kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda, kuma ta zargi gwamnatin Pakistan da mara mata baya.

Kasar ta Pakistan, wacce mamba ce a Kwamatin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar, ta sha musanta zargin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.