BBC navigation

Barack Obama ya kafa tarihi a Twitter

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 14:36 GMT

Kalmar "karin shekaru hudu" hade da hoton Barack Obama rungume da matarsa Michelle, ta zamo labarin da aka fi yadawa a tarihin shafin sada zumunta na Twitter.

Shugaban na Amurka ya aika sakon Twitter ne da misalin karfe 04:16 agogon GMT, inda jama'a suka rinka musayar sakon sau fiye da 500,000.

Wannan ya fito da gagarumar rawar da shafukan sada zumunta ke takawa wurin yada labarai da kuma shawo kan masu kada kuri'a.

A daidai lokacin da labarin nasarar Mr Obama, ya bazu, an aika sakonnin Twitter 327,452 masu alaka da labarin a kowanne minti guda.

obama

Wannan ne sako da Obama ya wallafa jim kadan bayan nasarar da ya samu

An kuma saka hoton a shafin Facebook, inda ya zamo hoton da ya fi jan hankalin jama'a a tarihin shafin na Facebook.

Sauran shugabannin duniya

Duka 'yan takarar biyu sun mayar da hankali sosai wurin yakin neman zabe a shafukan sada zumunta.

Haka ne ya sa 'yan Democrat suka rinka amfani da sakonnin email da Twitter wurin bayyana nasararsu ga magoya baya - tun kafin Mr Obama, ya yi jawabin amincewa da sakamakon zaben.

Sauran shugabannin duniya kamar David Cameron, na Burtaniya, sun yi amfani da wannan kafa wurin taya shugaba Obama murna.

"Ina taya abokina murna @BarackObama," kamar yadda Fira Ministan na Burtaniya ya rubuta a Twitter, wanda kuma aka yi musayarsa sau 1,500.

Sai dai duk da haka, kudaden da 'yan takarar biyu suka kashe wadanda sun haura dala biliyan daya wurin tallace-tallace a talabijin, sun yi fintinkau ga wadanda suka kashe a shafukan sada zumunta.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.