BBC navigation

An gabatar da wani kuduri da zai kara karfin iko ga shugaban kasar Turkiyya

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:18 GMT
Mr Recep Erdogan na Turkiyya

Kudurin kara karfin ikon shugaban Kasar Turkiyya

Jam'iyyar AK mai mulki a kasar Turkiya ta gabatarwa majalisar dokokin kasar wani kuduri da zai kara karfin iko ga shugaban kasar.

A kundin tsarin mulkin kasar a yanzu dai, shugaban Kasa ya kasance tamkar na jeka-na yika ne, a yayinda Firayim Minista ke da ikon zartar da manufofin gwamnati.

Firayim Minista mai ci, kuma shugaban jam'iyyar AK, Recep Tayyip Erdigan, ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a shekara ta 2014.

Shi dai mataimakin Firayim minista, Bekir Bozdag ya ce sauyin zai sa majalisar dokoki ta rage bata lokaci wajen tafka mahawara, a yayinda 'yan adawa suke cewar za a baiwa Mista Erdogan ikko fiye da kima.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.