BBC navigation

Ana ci gaba da zaɓen shugaban Amurka

An sabunta: 6 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:26 GMT

Rumfar zabe a Amurka

Yanzu haka miliyoyin Amurkawa na kaɗa ƙuri'unsu domin zaɓen shugaban ƙasa bayan da aka kwashe wata da watanni ana zazzafan yaƙin neman zaɓe mai tsadar gaske.

Fafatawar dai tafi zafi ne tsakanin Shugaba Barack Obama na jam'iyyar Democrat da kuma Mitt Romney na jam'iyyar Republican.

Shugaba Obama dai yana neman wa'adin mulki na biyu ne.

Jama'a kasahen duniya da dama dai na cigaba da bin diddigin zaben shugabancin kasar Amurkan, saboda irin rawar da kasar ke takawa a siyasar duniya.

Binciken jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa, Obama ya dan baiwa abokin hamayyar sa Mitt romney rata a jihohin da za a fafata a cikinsu

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.