BBC navigation

Angela Merkel ta kai ziyara ga Cameron

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:56 GMT

Angela Merkel

Shugabar gwmanatin Jamus, Angela Merkel, ta kai ziyara ga Firayin Ministan Birtaniya, David Cameron, a birnin London don samun amincewarsa game da kasafin kudin Tarayyar Turai na dogon lokaci.

Mista Cameron ya sha nanata cewa yana bukatar ganin an rage kasafin kudin Tarayyar Turai kuma ya yi barazanar hawa kujerar na ki game da duk wani kari a kasafin kudin.

Misis Merkel ba ta bayyana cewa za ta goyi bayan dakatar da duk wani kari kan kasafin kudin ba.

To amma ta ce bayar da wani wa'adi ba manufa ce mai kyau ba.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.