BBC navigation

'Yan tawaye na SPLM sun harbo wani jirgin yaki kusa da kan iyaka da Sudan ta Kudu

An sabunta: 8 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:38 GMT
Kordofan ta kudu

Rikici tsakanin Kordofan ta Kudu da Blue Nile ya tilastawa jama'a tserewa gidajen su

'Yan tawaye a jihar Kordofan ta Kudu dake Sudan, sun ce sun ce wani kakakin kungiyar 'yan tawaye ta SPLM -ta arewa, ya ce sun kakkabo jirgin yakin samfurin Antonov ne, bayan da su ka yi ta harbinsa da manyan bindigogi masu sarrafa kansu, a tsaunikan Nuba a jiya Laraba.

Sai dai har ya zuwa yanzu gwamnatin Sudan ba ta ce uffan a kan wannan ikirari ba.

'Yan tawayen dai su na yaki da gwamnatin kasar ta Sudan ne a yankin tun cikin watan Yunin bara.

Rikicin a jihar ta Kordofan ta Kudu da jihar Blue Nile, ya tilasta wa dubun dubatar jama'a ficewa daga gidajensu.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.