BBC navigation

Gabrielle ta yi ido hudu da wanda ya harbe ta

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:06 GMT

Gabrielle Giffords

Tsohuwar 'yar majalisar dokokin Amurka, Gabrielle Giffords, ta yi ido hudu da mutumin da ya harbe ta a ka, tare da kashe wasu karin mutane shida a wani gangamin siyasa da aka yi a kusa da wani babban shago a bara.

Misis Giffords ta na kotu aka shaidawa Jared Loughner cewa zai shafe sauran rayuwarsa a gidan yari, saboda harin da ya kai a Tucson na jihar Arizona.

Mijin Misis Giffords ya shaidawa kotun cewa, rayuwar mai dakinsa ta canza har abada, amma bai kashe mata karfin gwiwa ba.

Loughner, wanda ke da tarihin tabin hankali, ya amsa laifin da aka tuhume shi da aikatawa na kisa da yunkurin yin kisan.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.