BBC navigation

Burtaniya za ta daina baiwa Indiya tallafin kudi

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:00 GMT
David Cameron

Burtaniya za ta daina baiwa Indiya tallafin Kudi

Gwamnatin Birtaniya ta bayyana cewa, zata dakatar bada duk wani tallafin kudi ga India, saboda a cewar ta, yanzu lokaci ya yi da za'a dauki Indian a matsayin daya daga cikin Kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa.

Dama dai an jima ana cece-kuce a Birtaniya wacce ta yiwa Indian mulkin mallaka dangane da baiwa Indian tallafi, saboda irin arzikin da take da shi yanzu.

Wakilin BBC yace wannan mataki na dakatar da baiwa India duk wani tallafi, zai baiwa Birtaniya damar yin tsimin dala miliyan dari biyu da hamsin, wanda kadan ne kawai daga cikin makuden kudaden tallafi da Birtaniya take baiwa Kasashen duniya.

Gwamnatin Birtaniyan tace, nan da shekara ta 2015 ne zata dakatar da bada tallafin ga India.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.