BBC navigation

Obama zai kai ziyara Burma a karon farko

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:56 GMT

Shugaba Obama

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ba da sanarwar cewa Shugaba Obama shi ne zai zamanto shugaban Amurka na farko da zai kai ziyara kasar Burma a cikin wannan wata.

Shugaba Obama zai gana tare da shugaban Burman Thein Sein da jagorar 'yan adawar kasar Aung San Suu Kyi.

Wakiliyar BBC ta ce ziyarar ta Mista Obama ita ce kololuwar kokarin da gwamnatinsa ke yi na tsawon shekaru hudu don baiwa shugabannin kasar Burma kwarin gwiwar yin sassauci a harkokinsu.

Kasar Burma dai ta fara bin tafarkin dimokradiyya tafarkin da Obama yake ta basu kwarin gwiwa a kai.

Daidaito kan alakar kasashen za a iya cewa ya samu ci gaba tun bayan da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta kai ziyara kasar Burma a watan Dismabar bara.

Sai dai wasu 'yan Kungiyar kare hakkin biladama za su iya sukar ziyarar Mista Obama da cewa lokacin yinta bai yi ba, bisa la'akari da cewa dimokradiyyar a kasar na da shauran tafiya.

Gwamnatin Burma kuma ta gazawa ta hana barkewar rikici tsakanin yawancin mabiya addinin Budha da kuma Musulmi a yammacin kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.