BBC navigation

'Mutane fiye da dubu goma sha daya ne su ka tsere daga Syria cikin sa'oi 24'

An sabunta: 9 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 18:27 GMT
Syria

Jama'a na ci gaba da tserewa daga Syria

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tace mutane fiye da dubu goma sha daya ne suka tserewa Syria cikin sa'oi ashirin da hudu da su ka gabata kadai, a wata alama dake nuni da yadda rikicin kasar ya kazanta

Majalisar dinkin duniya tace Siriyawa dubu tara ne su ka tsallaka kan iyaka zuwa cikin Turkiyya domin gujewa fadan da ake yi a biranen Aleppo da Idlib

Wasu mutane dubu biyu kuma sun tsere zuwa kasashen Labanon da Jordan

Kungiyoyin bada agaji sun yi gargadin cewa gidajen da ake lalatawa da kayayyakin kiwon lafiya na dada karuwa

Sunce mutane fiye da miliyan biyu da rabi a cikin Kasar rabin su kananan yara, sun rasa mahallin su, kuma su na matukar bukatar taimako

Tunda farko dai Kamfanin dillacin labaru na Turkiyya yace jami'an Syria ashirin da shida da suka hada da manya manyan Janar na soji biyu sun sauya sheka daga bangaren dakarun Syria zuwa Turkiyya

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.