BBC navigation

Sababbin shugabanni za su karbi mulki a China

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:49 GMT
Xi Jinping

Xi Jinping a wajen taron Jam'iyyar Kwaminis ta China

Xi Jinping, dan kimanin shekaru 59 da haihuwa, ya kusa zama babban mai fada a ji, kuma shugaban da Jam'iyyar Kwaminis mai mulki ta zaba da zai shafe shekaru goma yana mulki.

Batun sauya shugabanni a China a kodayaushe na haifar da rudani. Sai dai kuma a yanzu kasar ta Sin ta kasance ita ce kasa ta biyu mafi bunkasar tattalin arziki a duniya kuma mai fada a ji a komai, saboda haka batun shugabancinta abin dubawa ne.

China dai na fuskantar kalubale da dama. Wasu masu sharhi sun yi amannar cewa bunkasar tattalin arzikin da ta ke samu yanzu yana da tangarda. Tambayar a nan ita ce, ta ya za a yi kasar da take bin tsarin jam'iyya daya za ta iya kaucewa son zuciya a tsarin gudanar da mulki?

Wani masanin tattalin arziki Mao Yushi ya ce "Abu ne mai wuyar gaske a ce mutane basu da 'yancin tofa albarkacin bakinsu idan sun ga gwamnati na abinda ta ga dama, ko da yake ba komai muka sani ba, amma mun san kadan daga cikin yadda gwamnatin ke tafiyar da mulkin ta."

Talakawa da mawadata

Shugabanin China dake mulkar kasar a yanzu karkashin jagorancin Hu Jintao, sun dare karagar mulki ne tun a shekarar 2002, kuma su ne karo na hudu tun bayan da jam'iyyar Kwaminis ta fara mulkin kasar a shekarar 1949.

Ya zamo wajibi su sauka, saboda shekarun wasu daga cikin shugabannin sun ja da yawa, ba za su iya wani abin a zo a gani ba.

A lokacin mulkin Hu Jintao dai tattalin arzikin kasar na karuwa da kashi 10 cikin 100 a duk shekara, lamarin da ya rage talauci a kasar. Amma daga bisani tattalin arzikin ya fara fuskantar tangarda.

"Bambancin da ke tsakanin talakawa da mawadata a bayyane ya ke karara, yanzu China ta zamo kasar attajirai, kodayake gwamnati ta kara inganta ayyukan kula da lafiya da kuma 'yan fansho"

Bambancin da ke tsakanin talakawa da mawadata a bayyane ya ke karara, yanzu China ta zamo kasar attajirai, kodayake gwamnati ta kara inganta ayyukan kula da lafiya da kuma 'yan fansho. Sai dai kuma hakan na fuskantar matsaloli da dama saboda a kodayaushe adadin mutanen kasar karuwa ya ke cikin sauri.

Fata da Fargaba

Masana sun ce ya kamata Mr. Xi ya bambanta kansa da magabatansa. Yana da karancin shekaru da fuskantar yanayin kasashen yamma. Sannan damar da ya samu na kasancewa da a wajen daya daga cikin manyan jami'an gwamnati zai ba shi damar tafiyar da ayyukansa yadda ya dace.

Sai dai wasu na ganin Mr. Xi wanda shi ma jam'iyyar kwaminis ce ta horar da shi, ba lallai bane ya sauya.

Jam'iyyar ta Kwaminis na da tarihin kawo sauye-sauye don ci gaba da zama kan karagar mulki.

Za ta iya gaggauta kawo sauye-sauye a fannin tattalin arzikin kasar dakuma warware damuwar da mutane ke nuna wa game da rashin daidaito a rabon arzikin kasa da kuma yaki da cin hanci.

Idan aka yi haka, ta yiwu Mr. Xi ya samu nasarar mika mulki ga wanda zai gaje shi a shekarar 2022.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.