BBC navigation

Daraktan CIA ya yi murabus

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:02 GMT

David Patraeus

Daraktan Hukumar leken asiri na kasar Amurka CIA David Petraeus, ya yi murabus, bayan da ya amince da neme nemen mata alhali da igiyar aure a kansa.

Shekara guda kenan da dan taki yayi akan wannan mukami, bayan aikin sojin da ya yi inda aka jinjina masa saboda nasarar da ya samu a Iraqi da Afghanistan.

Rahotanni dai na nuna cewa General Petraeus ya na neman wata mata ce wadda ke rubuta tarihinsa wato Paula Broadwell, wanda hukumar bincike ta Amurka FBI ta gano a lokacin da ta gudanar da wani bincike.

Wakiliyar BBC a Washington ta ce "Mr Petraeus ya ce halayyarsa a matsayinsa na mai aure kuma jagoran Hukuma kamar CIA, ya yi abin kunya."

Yanzu ya zama tilas kenan shugaba Obama ya sake zaben wani da zai jagoranci Hukumar wanda kuma majalisar dattawan kasar za ta tantance.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.