BBC navigation

Iraqi ta soke yarjejeniyar sayen makamai daga Rasha

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:15 GMT
Fira Minista Nouri al Maliki

Iraqi ta soke sayen makamai daga Rasha

Gwamnatin Iraqi ta soke wata yarjejeniyar sayan makamai ta dubban miliyoyin daloli tare da Kasar Rasha, saboda abinda Baghdad din tace damuwar da take dashi game shigar rashawa cikin yarjejeniyar

Wani mai magana da yawun Fira Ministan Iraqi Nouri al Maliki, yace yana da shakku game da shigar rashawa cikin yarjejeniyar, bayan wata ziyara da ya kai zuwa Moscow, a saboda haka ya yanke shawarar sake nazarin yarjejeniyar ta dala biliyan hudu da rabi

Yarjejeniyar samarwa da Iraqin makamai dai, da su ka hada da jiragen helicopta, za ta sa Rashan ta kasance kasa ta biyu mafi girma a duniya dake samar wa da Iraqin makamai, bayan Kasar Amurka

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.