BBC navigation

Yau ce ranar goyan bayan ayyukan Malala

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:06 GMT
Malala Yusufzai

Malala Yusufzai

Shugaban Pakistan Asif Ali Zardari yace gwamnatinsa zata kaddamar da wani sabon shiri na sanya karin miliyoyin yara- kanana a makaranta.

Iyalai matalauta a Kasar zasu rinka amsar kudi a kowanne wata daga gwamnati, idan suka sanya 'ya'yansu a makaranta.

Sanarwar dai na zuwa ne a ranar da majalisar dinkin duniya ta ware domin marawa ayyukan da Malala Yousufzai , wacce aka kai mata hari saboda gwagwarmayar da ta ke yi na ganin 'ya'ya mata sun sami ilmin bokon

Ms Choudhry wacce aka cire daga makaranta tana da shekaru 16, bayan an tilasta mata yin auren dole a Pakistan amma daga bisani ta koma makaranta, ta fadawa BBC cewa, idan har akwai wani daya cancanci karbar kyautar zaman lafiya ta Nobel ta gaba, to bata wuce Malala Yusuf zai ba.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.