BBC navigation

Baza ta sabu ba: Inji ma'aikatan PHCN

An sabunta: 10 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 15:23 GMT

A Najeriya, ma'aikatan hukumar samar da wutar lantarki ta kasar PHCN na ci gaba da kokawa bisa matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sayar da wasu bangarorin kamfanin.

Ma'aikatan dai sun ce suna nan kan bakar- su ta neman hakkokinkinsu kafin su amince a sayar da kamfanin ga 'yan kasuwa.

A baya dai gwamnatin Najeriyar ta ce tana tattauanawa tare da shugabannin kwadago na kamfanin domin samun dai-daito, dangane da kudadansu na fansho da suka ce sun da de suna tarawa, amma rana tsaka gwamnati ta ce zata mayar da kamfanin ga 'yan kasuwa, wanda hakan ke nufin kudadan nasu sun sha ruwa kenan.

Ko da yake ma'aikatan sun ce sun zauna sau daya kawai da bangaran gwamnatin domin samun maslaha, inda akai musu alkawarin sake zaunawa.

Sai dai kuma ba'a kai ga sake zaman bane suka ce sun ji gwamnatin ta fara sayar da wasu bangarori na kamfanin.

Lamarin da yasa yanzu ma'aikatan suka ce baza ta sabuba, har sai an biyasu hakkokinsu kafin su amince da sayar da kamfanin, in ko ba haka ba, za su dau matakin jefa baki dayan kasar cikin duhu.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.