BBC navigation

Ja'mian zabe a Florida sun ce Obama ne ya lashe zabe a Jihar

An sabunta: 11 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 05:56 GMT

Barack Obama

Jami'an zabe a Florida sun tabbatar da cewa Barack Obama ne ya lashe zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a ranar talatar da ta gabata a Jihar.

Nasarar ta sa da ya yi da kashi daya cikin dari ya kara tazararsa akan abokin karawarsa na Jami'yyar Republican Mitt Romney.

Wannan na nufin shugaba Obama ya samu nasara a jihohi takwas cikin jihohi tara masu matukar muhimmanci a zaben, kuma ya samu maki 332 a kuriun da aka kada, inda Mr Romney ya samu maki 206.

Shekaru goma sha biyu da suka gabata dai, an yi matukar takaddama game da sakamakon zaben Jihar Florida tsakanin George W Bush da Al Gore, sakamakon da aka yi amfani da shi wurin bayyana shugaban kasa.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.