BBC navigation

Manyan jami'an BBC sun sauka daga kan mukamansu

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 11:08 GMT
Helen Boaden

Helen Boaden ce daraktar labarai ta BBC lokacin da aka ki gabatar da wani shiri kan zargin Jimmy Savile

Daraktar labarai ta BBC, Helen Boaden, da mataimakinta sun "ja gefe" daga kan mukamansu har sai an kammala wani bincike na cikin gida.

Matakin da Mis Boaden da Steve Mitchell suka dauka dai ya biyo bayan murabus din Babban Daraktan BBC George Entwistle ne ranar Asabar.

Mista Entwistle ya yi murabus ne bayan wani rahoto da shirin talabijin na Newsnight ya bayar wanda ya kai ga zargin wani tsohon dan jam'iyyar Conservative mai mulki a Burtaniya bisa kuskure da aikata lalata da kananan yara.

Mista Entwistle ya kuma kafa wadansu kwamitoci guda biyu don su binciki shawarar da shirin na Newsnight ya yanke ta kin watsa wani rahoto a kan zargin tsohon mai gabatar da shirye-shirye na BBC Jimmy Savile da cin zarafin kananan yara. A bara ma'aikacin na BBC ya mutu aka kuma gabatar da shirye-shiryen ta'aziyyar mutuwarsa yayin bukukuwan Kirsimati da Sabuwar Shekara.

Ga na gaba...


Mis Boaden ce daraktar labarai ta BBC yayin da Mista Entwistle ke rike da mukamin daraktan talabijin lokacin da aka yanke shawarar kin yada zarge-zargen bara.

Mista Entwistle ya shaidawa Majalisar Dokoki ta Burtaniya cewa ya yi wata gajeruwar tattaunawa da Mis Boaden a kan binciken na Newsnight, amma bai tambaye ta karin bayani ba.

Tsohon shugaban gidan talabijin na Sky News Nick Pollard ne ke jagorantar daya daga cikin kwamitocin wanda aka dorawa alhakin gano dalilin da ya sa aka jingine binciken da aka kwashe makwanni shida ana gudanarwa a kan zarge-zargen.

An bukaci Mis Boaden da Mista Mitchell su sallama duk wata ragama da ke hannunsu a matsayinsu na shugaba da mataimakin shugaban Sashen Labarai na BBC, har sai kwamitin Pollard ya fitar da sakamakon bincikensa.

Mis Boaden ce ke da alhakin sa ido a kan daukacin labaran da ake yadawa a fadin Burtaniya da labaran duniya da al'amuran yau-da-kullum a radiyo, da talabijin, da intanet.

An bukaci Fran Unsworth, shugaban sashen nemo labarai, da Ceri Thomas, editan shirin Today na gidan radiyon BBC 4 su cike gurbinsu na dan wani lokaci.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.