BBC navigation

Majalisar Girka ta amince da kasafin kudin 2013

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:28 GMT

Zauren Majalisar dokokin Girka

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa ta 2013, wanda ya kunshi matakan zaftare kudade da kara tsuke bakin aljihu.

Ana dai kallon sabon kasafin kudin a zaman wani muhimmin yunkurin gwamnatin kasar na shawo kan masu ba ta rance domin su amince da ba ta wani sabon bashin zaburarda tattalin arziki.

Amincewar wadda ta samu rinjaye sosai, ta zo ne kwanaki kadan bayan wani shirin rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma kara haraji ya samu amincewar majalisar mai wakilai 300 da karamin rinjaye da bai kai na yanzun ba.

Wannan kuri'a dai yanzu ta bude wa Girkar wata kofar samun wani sabon bashin dala miliyan dubu arba'in na ceto tattalin arzikinta

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.