BBC navigation

Libya: An jinkirta shari'ar tsohon firayim minista

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 16:05 GMT

Al Baghdadi Al Mahmudi

Pira ministan karshe na gwamnatin Marigayi Kanar Gaddafi, watau Al Baghdadi Al Mahmudi ya bayyana na dan gajeren lokaci a gaban wata kotu dake Tripoli, babban birnin kasar Libya.

Kotun ta saurari shariar da ake ma shi ne na tsawon mintuna 10, amma baa karanta ma shi laifiufukan da ake tuhumar shi da su ba.

An shirya a watan gobe ne za'a cigaba da sauraren shariar.

Al Baghdadi alMahmudi ya gudu zuwa Tunisia mai makwabtaka a cikin watan Satumban bara, jim kadan bayan 'yan tawaye sun kama birnin Tripoli.

An tusa ƙeyarsa zuwa Libya ne a cikin watan Yunin da ya gabata, duk da damuwar da aka nuna cewa zai iya fuskantar azaba ko kuma hukuncin kisa.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.