BBC navigation

Ribadu: SERAP ta zargi gwamnatin Najeriya da yin nuku-nuku

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 09:02 GMT

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya ta nemi gwamnatin kasar da ta bayyana da kuma hukunta mutanen da rahoton Malam Nuhu Ribadu ya samu da laifi akan wadaka da kudaden man fetur.

A cikin wata sanarwa da ta aikowa BBC kungiyar ta zargi gwamnatin da yin wasu take-taken kaucewa aiwatarda rahoton domin rufawa wasu asiri.

Kungiyar tayi barazanar gurfanar da gwamnatin gaban kotu ,muddin ta ki daukar matakin hukunta mutanen.

To sai dai fadar shugaban kasar ta musanta yin watsi da rahoton ko kin daukar matakin hukunta wadanda aka samu da laifin.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.