BBC navigation

'yan adawar Syria sun hade wuri daya

An sabunta: 12 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 07:43 GMT
Syrian opposition

Gangamin 'yan adawar Syria

Bangarorin 'yan adawar Syria dake wani taro a birnin Doha na kasar Qatar, sun amince da kafa wata hadaddiyar kungiyar siyasa inda suka zabi wani mai wa'azin addinin musulunci a zaman shugaban kungiyyar.

Ana sa ran sabon kawancen ya samu daurin gindin kasashen Yamma da kuma kasashen da ke mara musu baya a yankin gabas ta tsakiya, da ke cikin kingiyar Friends of Syria Group.

Mutumin da aka nada a zaman shugaban sabuwar kungiyar shine Ahmad Mu'az Alkhatibi.

Hakama an nada wasu mutane biyu a zaman mataimakan sa da suka hada da Riad Seif, mutumin da ya kawo shawarar hadewar 'yan adawar karkashin shugabanci guda da kuma Suheir Al-attassi wata mata 'yar fafutuka; mai ra'ayin raba addini da siyasa.

Malami mai matsakaicin ra'ayi

Alkhatibi dai malamin addinin musulunci ne mai matsakaicin ra'ayi wanda ya bar birnin Damascus watannin uku kawai da suka wuce kuma saboda haka za a dauke shi a zaman wanda ke da masaniyar abubuwan ke gudana a cikin kasar.

Kungiyar kasashen da ke goyon bayan 'yan tawayen Syria da ake kira Friends of Syria group karkashin Jagorancin Amurka, ta yi alkawalin amincewa da kawancen a hukumance a zaman halattaciyar hukumar da ke wakiltar al'ummar Syria, kuma mai yiwuwa ne a bari ta karbi kujerar kasar Syria a Kungiyar kasashen Larabawa.

Kuma ana sa ran ta kafa wata gwamnatin rikon kwarya da kuma majalisar soji wadanda za su rika tsara yakin suke yi a fagen daga.

Tun ba yau ba dai kasashen yamma da abokan kawancensu sun nemi 'yan adawar da su hade wuri daya kana su samarwa magoya bayansu matattara daya.

Yanzu ga alama hakan ta samu, amma abin jira a gani shine ko akwai wani tasiri da hakan zai yi da kuma ko sabuwar kungiyar za ta samu goyon baya na zahiri.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.