BBC navigation

Yau talata ne za a sako Abu Qatada

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 06:00 GMT

Omar Uthman wanda aka fi sani da Abu Qatada

A yau ne za a saki malamin addinin Islaman nan mai ra'ayin sauyi Abu Qatada, bayan ya yi nasara a daukaka karar da ya yi, kan yunkurin da hukumomin Burtaniya ke yi na tasa keyarsa zuwa Jordan inda ake zarginsa da shirya kai hare-haren bam.

Za a dai sako Abu Qatada wanda ya kwashe shekaru bakwai yana kalubalantar yunkurin na mika shi ga gwamnatin Jordan ne daga wani babban gidan yari inda ake tsare dashi; amma bisa tsattsauran matakin hana shi walwala.

Sakin Malamin dai na zuwa ne a daidai lokacinda hukumomin kasashen Burtaniya da Kuma Jordan ke cigaba da nuna rashin amincewa da hukumcin da kotun musamman kan daukaka kararrakin da suka shafi shige -da-fice ta yanke kan batun tasa keyar tasa zuwa Jordan, inda ya zai fuskanci zarge- Zarge aikata ta'addanci.

Lauyoyinsa sun fadawa kotun ta musamman cewar ba zai samu a yi masa adilci a shara'a ba a kasar ta Jordan inda ake zarginsa da tsara kai hare-haren bom.

Tsaurara sharuddan beli

Abu Qatada wanda sunansa na ainihi Umar Uthman ya kwashe shekaru bakwai a daure a Burtaniya; kuma sakin da za a yi masa yau yana tare da tsauraran sharudda da suka hada da cewar yana da damar fita daga gidansa ne kawai tsakanin karfe takwas na safe zuwa karfe hudu na yamma.

Kuma dole ya saka wata naura a jikinsa sa'annan kuma za a rika kayyade masa mutanenda zai yi mu'amala da su.

Amma duk da hakan Sakatariyar Harkoki cikin gidan Birtaniyar Theresa May ta kira hukumcin a zaman wanda bai gamsar ba ko kadan don haka tace gwamnatin Burtaniya za ta kalubalanci hukumcin.

Theresa May ta baiyyana Abu Qatada a zaman wanda ake tuhuma da zama dan ta'adda kuma mutum mai hadari, don haka tace sam bata yarda da matsayin kotun ta musamman ba na amincewa da daukaka karar da yayi.

Kotu ta musamman dai tace bata gamsu da tabbacin da gwamnatin ta ba ta ba cewar ba za a yi anfani da duk wata shaida da aka samu daga azabtardashi a Jordan wajen yi masa shara'a a can ba.

Gwamnatin kasar Jordan dai ta ce za ta yi aiki tare da Birtaniya wajen ganin an mayarda Abu Qatada a kasar domin a sake yi masa shara'a.

A yanzu dai an cigaba da tattaunawa tsakanin mahukuntan kasashen biyu kan batun; kuma ana sa ran Sarkin Kasar ta Jordan ya ziyarci Birtaniya a makon gobe.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.