BBC navigation

Ba dalilin baiwa Entwistle albashin barin aiki - Cameron

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 08:16 GMT

George Entwistle, Darakta-Janar na BBC wanda yayi murabus

Gwamnatin Birtaniya da kuma jam'iyyun adawa a kasar sun yi Allah-wadai da shawarar baiwa tsohon Darakta Janar na BBC George Entwistle albashin ajiye aiki na fiye da dala dubu dari bakwai sakamakon murabus din da ya yi ranar Assabar.

Mista Entwistle ya sauka daga kan mukamin ne kwanakki 42 kawai da karbar shugabancin BBC, bayan watsa wani rahoto ta gidan talabijin wanda ya zargi wani tsohon dan majalisa da cin zarafin yara.

Firayin Ministan Burtaniya David Cameron ya ce abu ne mai wuya a kawo hujjar bashi ninkin abin da ya cancanci a ba shi; yayinda 'yan Majalisar Dokokin kasar daga jam'iyyar hamayya ta Labour suka ce bashi wadanan makudan kudin barin aiki yayi kama da bayar lada kan rashin samun nasara.

Sai dai Shugaban Hukumar BBCn wato BBC Trust, Lord Patten ya kare matakin na biyan George Entwinstle wadannan kudaden inda yace akwai hujjar yin hakan kuma dole ne ma domin ya tafi salun-alun da kuma a kaucewa samun abinda ya kira dogon tsaiko.

Kiran yin murabus

Sai dai 'yan majalisar Burtaniyar daga jam'iyyun Labour da kuma Conservative sun yi kira ga Lord Patten din da shi ma ya yi murabus saboda baiwa Mista Entwistle wadannan kudaden da kuma kasa shan kan wannan matsalar da ta taso.

George Entwisle dai ya bar shugabancin ne bayan da aka biya shi fan 450,000 abinda ke nufin an biya shi fam dubu takwas da dari uku da talatin da uku akan kowace rana daya ya yi rike da mukamin darakta Janar na BBC.

Rahotannin kafafen watsa labaran Birtaniyar sun ce hukumar kula da yadda ake kashe kudaden jama'a ta kasar za ta sake bitar biyan da aka yiwa tsohon shugaban na BBC bayan da firayin ministan kasar da kuma sakataren al'adu suka ce babu hujjar bashi wadannan kudaden.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.