BBC navigation

Amnesty: 'ana cin zarafin baki a Libya'

An sabunta: 13 ga Nuwamba, 2012 - An wallafa a 20:04 GMT

Tutar Libya

Wani rahoton kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International yace, 'yan kasashen wajen dake zaune a Libya na fuskantar hatsarin cin zarafi, da ci da guminsu, da ma lakada musu duka da tsare su har sai abinda hali yayi.

A cikin wata sanarwa kungiyar kare hakkin Bil Adaman ta ce sakamakon ziyarce-ziyarcen gani da ido da ta kai a Libyar tsakanin watan Mayu zuwa Satumba na bana, baki 'yan kasashen waje na fuskantar yiwuwar ci da guminsu da kuma kwadagon dole tare da kwace masu kudi.

Tun bayan tunɓuke gwamnatin marigayi Kanar Gaddafi ne dai ake zargin cin zarafin 'yan kasashen waje da tun farko 'yan tawayen Libya suka zarga da tallafawa Gaddafi wajen yakarsu.

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.